A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ana gabatar da jerin darussan Mahdawiyya mai taken "Zuwa Ga Al'umma Mai Manufa", da nufin yaɗa koyarwa da ma'arifar da suka shafi Imam Mahdi (A.F.).
(Ga wasu daga cikin ayoyin Alƙur'ani da suka shafi Imam Mahdi (A.F.) da juyin juya halinsa na duniya.)
Aya ta Huɗu
«وَ لِکُلٍّ وِجْهَةٌ هُوَ مُوَلّیها فَاسْتَبِقُوا الْخَیراتِ أَینَ ما تَکُونُوا یأْتِ بِکُمُ اللّهُ جَمیعًا إِنَّ اللّهَ عَلی کُلِّ شَیءٍ قَدیرٌ.»
"Kuma kowace al'umma tana da alkiblar da take fuskanta. Saboda haka ku yi gasa wajen aikata alheri. Duk inda kuke, Allah zai tattara ku gaba ɗaya. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai." (Suratul Baƙarah, aya ta 148)
Kowace al'umma tana da alkiblar da Allah Ya ƙaddara mata. Saboda haka kada ku yawaita gardama kan alkibla; a maimakon haka ku yi gasa wajen aikata alheri. Duk inda kuke, Allah zai tara ku gaba ɗaya domin saka wa nagari da azabtar da mugu a Ranar Alƙiyama. Lalle Shi Mai iko ne a kan komai.
A cikin ruwayoyi masu yawa daga Ahlul Baiti (A.S.), an fassara kalmar: "Duk inda kuke, Allah zai tattara ku gaba ɗaya" da tattaruwar sahabban Imam Mahdi (A.F.) a lokacin bayyanarsa.
Imam Muhammad Baƙir (A.S.) ya ce:
«یعْنِی أَصْحَابَ الْقَائِمِ الثَّلَاثَ مِائَةِ وَ الْبِضْعَةَ عَشَرَ رَجُلاً قَالَ وَ هُمْ وَ اللَّهِ الاُمَّةُ الْمَعْدُودَةُ قَالَ یجْتَمِعُونَ وَ اللَّهِ فِی سَاعَةٍ وَاحِدَةٍ قَزَعٌ کَقَزَعِ الْخَرِیفِ.»
«"Ana nufin sahabban Al-Qa'im ne, mutum ɗari uku da goma sha uku da wasu kaɗan. Na rantse da Allah, su ne 'al'umma ƙididdigaggu'. Na rantse da Allah, za su taru cikin sa'a guda kamar gutsattsarin gajimaren damina." (Al-Kafi, juzu'i na 8, shafi na 313)
Haka nan Imam Ali ar-Ridha (A.S.) ya ce:
«وَ ذَلِکَ وَ اللَّهِ أَنْ لَوْ قَدْ قَامَ قَائِمُنَا یجْمَعُ اللَّهُ إِلَیهِ شِیعَتَنَا مِنْ جَمِیعِ الْبُلْدَانِ.»
"Na rantse da Allah, idan Al-Qa'im namu ya tashi, Allah zai tattara mabiyanmu daga dukkan garuruwa zuwa gare shi." (Biharul Anwar, juzu'i na 52, shafi na 291)
Wannan fassarar tana daga cikin ma'anonin baɗinin aya, domin kamar yadda ruwayoyi suka bayyana, wasu ayoyin Alƙur'ani suna da ma'anoni masu yawa; wata ma'ana tana a fili kuma ta shafi kowa, yayin da ɗaya take ma'ana ta ciki wadda ba kowa ne yake sani ba face Manzon Allah (SAWA), Imamai (A.S.) da waɗanda Allah Ya so.
Dangane da waɗannan ruwayoyi, Allah Wanda yake da ikon tattara ƙwayoyin ƙasar da jikin mutane ya koma gare ta daga wurare daban-daban na duniya a Ranar Alƙiyama, cikin sauƙi Zai iya tattara sahabban Imam Mahdi (A.F.) cikin rana guda da sa'a guda domin kafa gwamnatin adalci ta duniya da kawo ƙarshen zalunci.
Aya ta Biyar
«بَقِیتُ اللّهِ خَیرٌ لَکُمْ إِنْ کُنْتُمْ مُؤْمِنینَ وَ ما أَنَا عَلَیکُمْ بِحَفیظ.»
"Abin da Allah Ya bar muku ya fi alheri gare ku idan kun kasance muminai. Kuma ni ba mai tsaronku ba ne." (Suratul Hud, aya ta 86)
Abin da Allah Ya bar muku daga halal ya fi alheri gare ku idan kuna da imani. Kuma ni ba mai tilasta ku yin imani ba ne.
A cikin ruwayoyi daban-daban an bayyana cewa "Baƙiyyatullah" yana nufin Imam Mahdi (A.F.) ko kuma wasu daga cikin Imamai (A.S.).
Imam Muhammad al-Bakir (A.S.) ya ce:
«وَ أَوَّلُ مَا ینْطِقُ بِهِ هَذِهِ الْآیةُ «بَقِیتُ اللَّهِ خَیرٌ لَکُمْ إِنْ کُنْتُمْ مُؤْمِنِینَ» ثُمَّ یقُولُ: أَنَا بَقِیةُ اللَّهِ فِی أَرْضِه.»
"Abu na farko da Imam Mahdi (A.F.) zai faɗa bayan bayyanarsa shi ne wannan aya: 'Baƙiyyatullahi khairun lakum in kuntum mu'minin.' Sannan zai ce: 'Ni ne Baƙiyyatullah a bayan ƙasa.'" (Kamaluddin wa Tamamun Ni'imah, juzu'i na 1, shafi na 330)
Hakika a cikin wannan aya ana magana ne da mutanen Annabi Shu'aibu (A.S.), kuma abin da ake nufi da "Baƙiyyatullah" shi ne riba da dukiyar halal ko kuma ladan Allah. Amma duk wata halitta mai amfani da Allah Ya bari domin amfanin mutane kuma ta zama hanyar alheri da farin ciki, ana iya kiranta Baƙiyyatullah.
Saboda haka, dukkan Annabawan Allah da manyan shugabanni su ma Baƙiyyatullah ne.
Tun da Imam Mahdi (A.F.) shi ne shugaba na ƙarshe kuma mafi girman jagora bayan aiko Manzon Allah (SAWA), yana daga cikin mafi bayyana kuma mafi cancantar misalan Baƙiyyatullah, musamman kasancewarsa shi kaɗai ya rage bayan Annabawa da Imamai.
Aya ta Shida
«هُوَ الَّذی أَرْسَلَ رَسُولَهُ بِالْهُدی وَدینِ الْحَقّ ِ لِیظْهِرَهُ عَلَی الدِّینِ کُلِّهِ وَلَوْ کَرِهَ الْمُشْرِکُونَ.»
"Shi ne Wanda Ya aiko Manzonsa da shiriya da addinin gaskiya domin Ya rinjayar da shi a kan dukkan addinai, ko da mushrikai sun ƙi." (Suratut Tauba, aya ta 33)
Wannan aya ta zo da irin wannan lafazi a Suratus Saff, sannan ta sake zuwa da ɗan bambanci kaɗan a Suratul Fath. Tana ba da labarin wani babban al'amari, kuma muhimmancin wannan al'amari ne ya sa aka maimaita ta. Tana sanar da yaɗuwar Musulunci a duk faɗin duniya da rinjayarsa a kan sauran addinai.
Wasu masu tafsiri sun ɗauki wannan rinjaya a matsayin rinjaya ta wani yanki kawai, wadda ta faru a zamanin Manzon Allah (SAWA) ko bayan haka. Amma kasancewar ayar ba ta ƙuntata wannan ma'ana da wani sharadi ba, babu dalilin taƙaita ta.
Ma'anarta ita ce cikakkiyar rinjayar Musulunci a kan dukkan addinan duniya; wato a ƙarshe Musulunci zai mamaye dukkan doron ƙasa kuma ya yi rinjaye a kan duniya baki ɗaya.
Babu shakka wannan bai kammala faruwa ba tukuna, amma wannan alkawarin tabbatacce na Allah yana ci gaba da cika sannu a hankali. Bisa ga ruwayoyi, cikakken cikar wannan shiri zai kasance ne lokacin da Imam Mahdi (A.F.) zai bayyana ya kuma tabbatar da yaɗuwar Musulunci a duniya baki ɗaya.
Sheikh Saduk (R.A.) ya ruwaito daga Imam Ja'afar al-Sadiq (A.S.) a tafsirin wannan aya cewa:
«وَ اللَّهِ مَا نَزَلَ تَأْوِیلُهَا بَعْدُ وَ لَا ینْزِلُ تَأْوِیلُهَا حَتَّی یخْرُجَ الْقَائِمُ عجل الله تعالی فرجه الشریف فَإِذَا خَرَجَ الْقَائِمُ لَمْ یبْقَ کَافِرٌ بِاللَّهِ الْعَظِیمِ وَ لَا مُشْرِکٌ بِالْإِمَامِ إِلَّا کَرِهَ خُرُوجَهُ حَتَّی لَوْ کَانَ کَافِرٌ أَوْ مُشْرِکٌ فِی بَطْنِ صَخْرَةٍ لَقَالَتْ یا مُؤْمِنُ فی بَطْنِی کَافِرٌ فَاکْسِرْنِی وَ اقْتُلْهُ.»
"Na rantse da Allah! Har yanzu cikakken tawilin wannan aya bai bayyana ba, kuma ba zai bayyana ba har sai Al-Qa'im (A.F.) ya fito. Idan ya bayyana, ba wani kafiri da ya kafircewa Allah ko mai musun Imami da zai rage face zai ƙi fitowarsa. Ko da wani kafiri ya ɓoye a cikin dutse, dutsen zai ce: 'Ya kai mumini! A cikina akwai kafiri; karya ni ka kashe shi.'" (Kamaluddin wa Tamamun Ni'imah, juzu'i na 2, shafi na 670)
Wasu malaman Shi'a sun ambaci cewa adadin ayoyin Alƙur'ani da suka shafi Mahdawiyya ya haura 120, kuma ana iya komawa ga manyan littattafan da suka yi bayani dalla-dalla kan wannan fanni. Saboda haka, a nan za mu takaita da wannan adadi na ayoyin Mahdawiyya.
Wannan tattaunawa za ta ci gaba...
An ciro daga littafin "Darsnameh Mahdaviyyat", wanda Khudamurad Salimiyan ya rubuta, tare da ɗan gyara kaɗan
Ra'ayinka